Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Xi ya gana da kantomar yankin musammam na HK
2019-11-05 09:40:54        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana a jiya Litinin, da kantomar yankin musammam na HK Carrie Lam, wadda ke birnin Shanghai domin halartar baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na 2.

Bayan sauraron rahoton kantomar game da yanayin da ake ciki a HK, shugaba Xi ya ce, rikicin dake wakana a yankin ya shafe watanni 5. Kuma Carrie Lam ta jagorancin gwamnatin yankin wajen sauke nauyin dake wuyanta da kokarin shawo kan rikicin da inganta yanayin zaman al'umma, kuma ta yi aiki tukuru.

Shugaba Xi ya kuma bayyana cewa, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ta aminta da kantoma Carrie Lam da ayyukan da ita da jami'an gwamnatinta suke yi. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China