Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministan Sin ya tashi zuwa Uzbekistan da Thailand
2019-11-01 11:36:05        cri

A yau Jumma'a ne firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya tashi daga birnin Beijing domin fara ziyarar aiki a kasashen Uzbekistan da Thailand, bisa gayyatar da takwarorinsa na Uzbekistan Abdulla Aripov, da na Thailand Prayut Chan-o-cha suka yi masa.

Yayin ziyarar ta wannan karo, ana sa ran Mr. Li zai halarci taro na 18 na firaministocin kasashen kungiyar hadin kai ta Shanghai, wanda zai gudana a birnin Tashkent fadar mulkin Uzbekistan. Zai kuma halarci taron shugabanni na 22 na Sin da kasashe mambobin kungiyar ASEAN, da taro na 22 na Sin da kasashe mambobin ASEAN, da Japan da Koriya ta Kudu. Kaza lika zai halarci taro na 14 na kasashen gabashin Asiya, wanda zai gudana a birnin Bangkok fadar mulkin kasar Thailand. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China