Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang zai ziyarci kasashen Uzbekistan da Thailand
2019-10-25 20:48:31        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Madam Hua Chunying ta bayyana yau Jumma'a cewa, bisa goron gayyatar da takwarorinsa na kasashen Uzbekistan da Thailand suka ba shi, firaministan kasar Sin Li Keqiang zai halarci taro na 18 na majalisar shugabannin gwamnatocin kasashe membobin kungiyar hadin-kai ta Shanghai wanda za'a yi daga ranar 1 zuwa 5 ga wata mai zuwa a birnin Tashkent, inda kuma zai yi ziyarar aiki kasar ta Uzbekistan, baya ga haka, zai halarci wasu jerin muhimman taruka a birnin Bangkok na kasar Thailand, ciki har da taro na 22 na shugabannin kasar Sin da kasashen kungiyar ASEAN, da taro na 22 na shugabannin kasashen ASEAN da kasashen Sin da Japan da Koriya ta Kudu, gami da taron koli na gabashin Asiya karo na 14 ko kuma EAS a takaice, tare da yin ziyarar aiki kasar Thailand.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China