Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ba za a taba mantawa da gudummuwar baki kwararru ba
2019-10-01 10:10:59        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya ce al'ummar Sinawa ba za su taba mantawa da gudummuwar da baki kwararru suka bayar ga ci gaban kasar Sin cikin shekaru 70 tun bayan kafa Jamhuriyar jama'ar kasar ba.

Li Keqiang ya bayyana haka ne jiya Litinin a dakin taron jama'a na birnin Beijing, lokacin da ya gana da tawagar kwararru 'yan kasashen waje da suka samu lambar karramawa ta abota, wadda gwamnatin kasar Sin ke bayarwa a kowacce shekara, ga baki mazauna kasar da suka taka rawar gani.

Ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da fadada hadin gwiwa da kasashen waje a fannin kirkire-kirkiren fasaha da kara samar da ayyuka a fannin kimiyya da fasaha ga baki kwararru da karfafa musu gwiwar shiga shirye-shiryen kimiyya da fasaha na kasar.

A nasu bangaren, bakin da aka karrama, sun godewa Firaministan da gwamnatin kasar Sin, sannan sun taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar Jamhuriyar jama'ar Sin, inda kuma suka ce za su ci gaba da yin kyakkyawan tasiri a fannin zamanantar da kasar Sin da ci gaban al'ummar kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China