Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Firaministocin Sin da Pakistan sun yi shawarwari
2019-10-09 11:11:16        cri

Jiya Talata ne firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi shawarwari da takwaransa na kasar Pakistan Imran Ahmed Khan Niazi a nan Beijing, inda ya jaddada cewa, kasar Sin na bada muhimmanci sosai ga huldar dake tsakaninta da Pakistan, kuma tana son hada hannu da Pakistan wajen raya hulda da hadin gwiwarsu zuwa sabon mataki. Kana sun gane ma idonsu bikin daddale yarjejeniyoyi da dama kan hadin gwiwar kasashen biyu a fannonin raya ababen more rayuwar jama'a, aiwatar da dokoki, tsaro, al'adu, ilmi, kafofin yada labaru da dai sauransu.

A yayin shawarwarin, Li Keqiang ya ce, kasar Sin na son ci gaba da taimakawa Pakistan gwargwadon karfinta, wajen inganta hada manyan tsare-tsarensu na raya kasa tare, da kyautata hadin gwiwarsu a fannonin raya ababen more rayuwar jama'a, tattalin arziki, ciniki, hada-hadar kudi, kera kayayyaki da dai sauransu.

A nasa bangaren, Imran Ahmed Khan Niazi ya taya jamhuriyar jama'ar kasar Sin murnar cika shekaru 70 da kafuwa. Ya kuma nuna cewa, sakamakon taimakon kasar Sin da goyon bayanta, Pakistan tana farfado da tattalin arzikinta yadda ya kamata. Ya ce Kasarsa tana son hada kai da Sin wajen gaggauta aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya". Tana kuma mai da hankali kan bunkasa hanyar raya tattalin arziki a tsakanin Sin da Pakistan da tashar jiragen ruwa ta Gwadar, kana tana son yin kokari da kasar Sin wajen kara zuba wa juna jari ta fuskar ciniki, domin raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 gaba. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China