Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang ya gana da Vladimir Putin
2019-09-19 10:21:34        cri
Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a yammacin jiya Laraba a fadar Kremlin dake Moscow.

A yayin ganawar, Li Keqiang ya bayyana cewa, kasarsa na son kara karfafa dankon zumunci, da zurfafa hadin kai da mu'amala tare da bangaren Rasha. Ya ce kasar Sin za ta kiyaye tsarin cinikayya tsakanin bangarori daban-daban karkashin jagorancin MDD bisa tushen ka'idojin kungiyar WTO, wannan na da ma'ana kwarai wajen inganta ci gaba da wadata da zaman lafiyar duniya.

A nasa bangaren, shugaba Vladimir Putin ya taya Jamhuriyar jama'ar kasar Sin murnar cika shekaru 70 da kafuwa, a cewarsa, huldar dake tsakanin kasashen Rasha da Sin na da muhimmanci sosai wajen kiyaye dangantakar kasa da kasa. Ya kara da cewa, kasarsa tana son hade dabarun ci gabanta da shawarar "Ziri daya da hanya daya", da kuma kara habaka fannonin cinikayya a tsakanin bangarorin biyu, don neman ci gaba tare.

Li Keqiang ya iso Moscow daga Saint Petersburg, bayan kammala shawarwarin firaministocin kasashen biyu karo na 24 da aka saba yi. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China