Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang: Sin na maraba da kasa da kasa ciki hadda Amurka da su kara zuba jari a kasar Sin
2019-10-17 20:57:40        cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya bayyana a yau Alhamis a nan birnin Beijing cewa, Sin za ta kara bude kofarta ga ketare, kuma tana maraba da kasa da kasa ciki hadda Amurka da su habaka zuba jari ga juna, ta yadda za su hadin kai da cin moriya tare.

A yau ne Li ya gana da tawagar wakilan Amurka karkashin jagorancin Evan Greenberg, shugaban majalisar zastaswar kungiyar 'yan kasuwar Amurka da Sin na kasar Amurka.

A nasa bangare, wakilan Amurka sun nuna cewa, hadin kan kasashen biyu ya dace da muradun kasashen biyu baki daya. 'Yan kasuwar Amurka na fatan ci gaba da tuntubar kasar Sin, kuma ba su son ganin Sin da Amurka sun katse huldarsu ko kadan, kuma sun nuna rashin jin dadi kan takadammar ciniki da kara sanya haraji da suke yiwa juna. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China