Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran za ta dawo teburin shawarwari da Amurka idan zai dace da moriyar kasa, in ji Rouhani
2019-10-15 13:31:21        cri
Jiya Litinin, shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana a yayin taron manema labarai da aka yi a fadar shugaban kasar cewa, ko kasar Iran da kasar Amurka za su dawo teburin yin shawarwari ya danganta da moriyar kasar Iran, ba wai batun wane ne a kan mulkin shugabancin kasar Amurka ba.

Mr. Rouhani ya ce, idan kasar Amurka ta soke takunkumin da ta kakabawa kasar Iran, kasar Iran za ta so dawo wa kan teburin yin shawarwari kan batun nukiliyar kasar bisa yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma. Kuma ya kamata shawarwarin da za su yi ya dace da moriyar kasar ta Iran, ba za ta canja matsayinta ba sabo da binciken neman tsige shugaban kasar Amurka da take yi a halin yanzu, ko kuma sakamakon babban zaben shugaban kasar Amurka da za a yi a shekarar 2020, watau, duk wanda ya zama shugaban kasar Amurka, kasar Iran ba za ta canja wannan matsayi ba.

Da yake tsokaci kan dangantakar dake tsakanin kasar Iran da kasar Saudiya, shugaba Rouhani ya ce, kasar Iran tana son warware sabanin dake tsakaninta da kasar Saudiya ta hanyar yin shawarwari. Za ta kuma ci gaba da yin bincike kan harin da aka kai kan jirgin ruwan dakon mai na kasar Iran a bahar Maliya dake kusa da kasar Saudiya, kuma har yanzu ba ta gano wadanda suka kai wannan hari ba. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China