Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Iran ya ce babu wata tattaunawa tsakaninsa da Amurka matukar bata dage takunkumin da ta kakabawa kasarsa ba
2019-09-26 11:47:06        cri
Shugaban Iran Hassan Rouhani, ya soke duk wani batun tattaunawa da Amurka, matukar bata dage takunkumin da ta kakabawa kasarsa ba.

Yayin muhawarar babban zauren MDD a jiya, Shugaba Rouhani ya ce a madadin kasarsa, zai sanar da cewa martaninsu ita ce, duk wata tattaunawa karkashin takunkumi ba zai yuwu ba.

Ya ce yanzu a bayyane yake cewa, MDD ta juyawa kudurinta baya, sannan Turai ma ta gaza kuma ba zata iya cika nata alkawarin ba. Ya ce suna nan a kan bakansu na cika alkawarin da suka dauka cikin yarjejeniyar nukiliyar kasar, sai dai, hakurinsu na da iyaka.

A watan Yulin 2015 ne Iran ta cimma yarjejeniyar da Birtaniya da Sin da Faransa da Jamus da Rasha da kuma Amurka, wadda nan take kudurin kwamitin sulhu na MDD mai lamba 2231 ya amince da ita. Sai dai, a watan Mayun bara, Amurka ta janye daga yarjejeniyar tare da sake kakabawa Iran din takunkumi, lamarin da ya sa Tehran ta ki cika alkawuran da ta dauka cikin yarjejeniyar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China