Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban kasar Iran ya yi kira ga kasa da kasa da su yi watsi da ra'ayin bangare daya na kasar Amurka
2019-10-02 16:37:16        cri
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya bayyana a birnin Erevan na kasar Armenia a jiya cewa, ya kamata kasa da kasa su yi watsi da ra'ayin bangare daya na kasar Amurka.

An gudanar da taron majalisar kwamitin tattalin arzikin Turai da Asiya a birnin Erevan a jiya, shugaba Rouhani ya halarci taron tare da yin jawabi bisa gayyatar da aka yi masa. Bisa labarin da aka bayar a tashar internet ta watsa labaru ta kasar Armenia, Rouhani ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, tilas ne dukkan kasashen duniya su ki amincewa da ra'ayin bangare daya, da daukar alhakin tabbatar da zaman lafiya da na karko da kuma odar duniya tare.

Shugaba Rouhani ya ce, manufofin kasar Amurka na yin matsin lamba ga kasar Iran sun fara kawo illa ga moriyar jama'ar kasar Iran, kana ya yi kira ga kasa da kasa da su dauki matakai don kin amincewa da ra'ayin bangare daya na kasar Amurka. Ya kara da cewa, bisa yanayin da ake ciki a duniya, sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban ita ce kawai hanya mafi dacewa. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China