Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ambaliya ta rutsa da sama da kauyuka 100 a arewa maso gbashin Nijeriya
2019-10-29 13:48:57        cri

Sama da kauyuka 100 na jihar Adamawa dake yankin arewa maso gabashin Nijeriya ne ambaliyar ruwa ta rutsa da su, saboda ruwan sama akai akai da aka fuskanta a yankin.

Da yake tabbatar da batun ga manema labarai, shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar, Muhammad Sulaiman, ya bayyana yanayin ambaliyar a matsayin mafi muni da jihar ta fuskanta.

Ya ce ana kokarin ceto mutane a kauyukan da ambaliyar ta rutsa da su, ciki har da tura 'yan sandan ruwa domin ceto mutane a kauyuka masu nisa da ambaliyar ta shafa a kan gabar kogin Benue.

Ya ce kawo yanzu, gwamnati ta kafa sansanoni 6 na 'yan gudun hijira ga wadanda lamarin ya shafa, yana mai cewa za a kafa wasu karin sansanonin a sauran yankunan da iftila'in ya shafa.

Tun a farkon watan Augusta, hukumar kula da yanayi ta kasar, wadda ke da alhakin yin gargadin ambaliya, ta fitar da gargadi game da yiwuwar fuskantar ambaliya, saboda ruwan sama mai karfi a fadin kasar.

Hukumar ta yi hasashen cewa, a bana, dukkan jihohi 36 na kasar da birnin tarayya Abuja, za su fuskanci ambaliyar ruwa a matakai daban daban. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China