Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sabon rikici a Nigeria ya raba mutane sama da 140,000 da gidajensu a 2019
2019-10-26 15:55:56        cri
Stephane Dujarric, Kakakin Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce sabon rikici a bana, da galibi kungiyar Boko ta haifar, ya tilasta raba mutane sama da 140,000 da gidajensu a yankin arewa maso gabashin Nigeria.

Stephane Dujarric, ya ce ayyukan ta'addanci ya kara yawaita adadin mutanen da suke barin gidajensu a jihar Borno, inda a bana kadai, mutane sama da 140,000 suka bar gidajensu. Ya na mai cewa galibin manoma sun yi asarar lokutan noma, kuma sama da mutane miliyan 3 na fuskantar rashin abinci.

Ya kara da cewa, tun farkon barkewar rikicin, MDD da abokan huldarta ke taimakawa wajen aiwatar da ayyukan jin kai a arewa maso gabashin Nijeriya, yana mai cewa, a 2019 kadai, sun samar da kayyakin ceton rai ga sama da mutane miliyan 3.8.

Sai dai, Stephane Dujarric ya ce yanzu haka, sama da mutane miliyan 7 suna bukatar taimakon jin kai a jihohin Borno da Adamawa da Yobe. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China