Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
A kalla mutane miliyan 2 da rikici ya raba da muhallansu ne suka koma gida a yankin arewa maso gabashin Najeriya
2019-10-24 20:36:06        cri
Mataimakin babban sakataren MDD mai kula da harkokin jin kai Mark Lowcock ya bayyana cewa, a kalla mutane miliyan biyu da rikici ya raba da muhallansu a yankin arewa maso gabashin Najeriya ne, suka koma gida.

Jami'in wanda ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ya ce, an samu wannan nasara ce, sakamakon matakan da sojoji ke dauka a yankin. Hakan a cewarsa, ya biyo bayan matakan da gwamnatin Najeriya da sojoji da kungiyoyin bayar da agaji ke dauka, don kawo karshen kuncin da jama'a suka dade suna fama da shi, sakamakon ayyukan ta'addanci na mayakan Boko Haram. (Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China