Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 7 sun mutu a wani hadarin motar tawagar gwamna a Najeriya
2019-10-20 16:44:17        cri
Mutane 7 ciki har da kananan yara 2 ne suka mutu a wani hadarin mota da ya rutsa da tawagar gwamna a Najeriya da sanyin safiyar Asabar a kudancin kasar.

Hukumar 'yan sandan yankin ta tabbatar da faruwar lamarin, tace al'amarin ya faru ne a babbar hanyar motar Benin zuwa Auchi dake jahar Edo a kudancin kasar, kana wasu mutanen uku sun samu raunuka.

Wata motar jami'an tsaro dake cikin ayarin gwamna Godwin Obaseki, na jahar Edo, tayi taho mu gama da wata mota dake tahowa ta gabansu a yayin da gwamnan ke han hanyar zuwa wani taro, in ji jami'in 'yan sandan.

Danmallam Mohammed, kakakin hukumar 'yan sandan jahar Edo, ya bayyana al'amarin da cewa abin bakin ciki ne.

Ya kara da cewa, tuni aka garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa asibitin Benin City, babban birnin jahar don duba lafiyarsu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China