Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bakin haure 141 ne suka nemi komawa Nijeriya daga Libya bisa radin kansu
2019-10-26 16:25:56        cri
Hukumar kula da masu kaura ta duniya (IOM), ta ce ta kwashe bakin haure 141, wadanda suka nemi komawa gida da kansu, daga Libya zuwa Nijeriya.

Cikin wata sanarwa, hukumar IOM ta ce ta taimaka wajen kwashe bakin haure 141 'yan asalin Nijeriya dake watangarari a Libya cikin jirgin shata daga filin jirgin saman Sebha na Libyar, kuma bakin hauren ne suka nemi komawa gida da kansu.

Sanarwar ta ce bakin hauren sun hada da maza 55 da mata 42 da yara 33 da kuma kananan yara 11. Kuma daga cikinsu, akwai marasa lafiya 13, ciki har da mata masu ciki 5.

Kwashe bakin hauren, wani bangare ne na shirin hukumar na mayar da bakin hauren dake watangarari a Libya, wadanda kuma suka nemi komawa gida, kasarsu na asali.

A cewar hukumar, akwai sama da bakin haure 650,000 a Libya, ciki har da kimanin 6,000 dake tsare a cibiyoyin da ake tsugunarsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China