Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban bankin Najeriya ya sha alwashin dakile hauhawar farashi a kasar
2019-10-20 16:43:34        cri
Babban bankin Najeriya yace zai cigaba da daukar kwararan matakan tafiyar da manufofin kudi domin hana tashin farashin kayayyaki a kasar.

Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya bayyana hakan ne a lokacin gabatar da rahoton babban bankin game da daidaita harkokin kudaden kasar na shekarar 2018, wanda aka baiwa kwafin sanarwa ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a Legas a jiya Asabar.

A cewar rahoton baya bayan nan na hukumar kididdiga ta kasar wato NBS, farashin kayayyaki a kasar ta yammacin Afrika ya karu da kashi 11.24 a watan Satumbar 2019, inda ya karu da 0.22 idan an kwatanta da watan Augasta.

Game da matakin karfin tattalin arzikin GDP kuwa, Emefiele yace, matsayin GDPn ya karu, hakan kuwa ya biyo bayan nasarorin da aka samu ne wajen fadada hanyoyin kudaden shiga wadanda basu shafi albarkatun man fetur ba, a yunkurin da gwamnatin Najeriyar ke yi na fadada tattalin arzikin kasar da kuma bunkasa hanyoyin samun kudaden shigar kasar.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China