Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An yi bikin baje kolin shimfidar wurin kasar Sin ta fasahar VR a Nijeriya
2019-10-19 15:50:36        cri

 

An yi bikin baje kolin yanayin shimfidar kasar Sin ta fasahar VR mai wa'adin mako daya a cibiyar al'adun kasar Sin dake Abuja, fadar mulkin Nijeriya, inda fasahar VR ta baiwa 'yan Nijeriya damar ganewa idonsu shimfidar kasar Sin, tamkar sun ziyarci kasar.

Cibiyar yada al'adun kasar Sin dake Nijeriya da hadin gwiwar cibiyar musayar al'adun Sin da ketare da kuma cibiyar yada labarai ta Wuzhou ne suka gabatar da wannan biki, da zummar yin amfani da fasahar VR don bayyana shimfidar kasar Sin masu kayatarwa, ta yadda mahalarta bikin za su fahimci al'adu da yanayin shimfidar kasar Sin sosai. Mutane fiye da dari sun halarci biki, ciki hadda karamin jakadan Sin mai kula da harkokin al'adu, kana direktan cibiyar al'adun kasar Sin Li Xuda, da kuma masanan Nijeriya a fannin al'adu, fasahohi da ilmi da kuma jami'an diplomasiyya na kasar Switzerland da Masar da dai sauransu, har ma da daliban kwalejin dangantakar kasa da kasa na jami'ar Abuja, kana da dalibai masu koyon Sinanci a cibiyar da dai sauransu.

Ban da fasahar VR, an kuma gabatar da bikin wasan kayayyakin kida na gargajiya na kasar Sin mai taken "Saurari kasar Sin" da bikin nuna kayayyakin wasa na fifilo masu salon kasar Sin, abubuwan da suka ja hankalin mahalarta taron sosai.

 

An ce, aikin bayyana yanayin shimfidar kasar Sin ta fasahar VR da cibiyar yada labarai ta Wuzhou ta gabatar, ya kasance irinsa na farko don yayata al'adun yawon shakatawa na kasar Sin ga ketare bisa wannan fasaha. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China