Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta bayyana wasu iftilain da ake fama da su a kasashen Afrika
2019-10-29 11:04:31        cri

MDD ta bayyana wasu iftila'i masu alaka da yanayi da ake fama da su a kasashe da dama na Afrika, daga ambaliya a kasashen Somalia da Sudan ta Kudu, zuwa fari a kasar Zambiya.

Farhan Haq, mataimakin kakakin Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya bayyana yayin taron manema labarai a jiya cewa, lokacin damina ya fara da wuri a wasu sassa na Somalia, wanda ya kai ga ambaliya a jihohin Hirshabelle da Jubaland da yankin kudu maso yammacin kasar, yana mai cewa, an yi kiyasin sama da mutane 180,000 sun rasa matsugunansu.

Ya kara da cewa, tun daga watan Yulin bana, aka samu matsananciyar ambaliyar ruwa a Sudan ta Kudu, lamarin da ya lalata yankunan kasar da dama. Ya kuma yi kiyasin ambaliyar ta shafi mutane 900,000.

A Zambiya kuma lamarin ya sha bambam, inda kasar ke fuskantar rashin ruwan sama.

A cewar Farhan Haq, MDD da abokan huldarta, sun kaddamar da aikin ba da agajin jin kai na watanni 7, domin magance bukatun agaji dake karuwa saboda mafi karancin ruwan sama da kasar ta fuskanta tun daga shekarar 1981. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China