Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Afrika ta kudu ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sin
2019-10-19 15:47:00        cri

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa ya gana da mamban majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, a jiya Juma'a a birnin Durban.

Yayin ganawar tasu, Cyril Ramaphosa ya ba da sakon gaisuwa da fatan alheri zuwa ga shugaban kasar Sin, Xi Jinping. Ya kara da cewa, Afrika ta kudu na ba dangantakar abota bisa manyan tsare-tsare dake tsakaninta da kasar Sin muhimmanci, yana mai godiya da taimako mai karfi da gwamnatin Sin ke ba kasarsa. Ya ce Afrika ta Kudu na daukar zumunci da amincin dake tsakaninsu da muhimmanci, yana mai fatan kasashen 2 za su marawa juna baya kan muradunsu da wasu manyan batutuwan dake jan hankalinsu baki daya. Har ila yau, Cyril Ramaphosa ya ce, kasarsa na fatan kara yin musanyar ra'ayi da kasar Sin kan dabarun gudanar da harkokin kasa, da kuma hada ci gaban kasar da aikin raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" waje guda, ta yadda za a ingiza dangantakar Sin da Afrika ta kudu zuwa wani sabon matsayi. Ya ce, a halin yanzu dai, Afrika ta kudu da kasar Sin na hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da kara tuntubar juna karkashin tsarin MDD da kungiyoyin G20 da BRICkS, don kyaye moriyar kasashe masu tasowa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China