Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan marasa aikin yi a kasar Afrika ta Kudu ya karu zuwa kaso 29
2019-07-31 10:09:46        cri
Hukumar kididdiga ta kasar Afrika ta kudu, ta ce adadin marasa aikin yi a kasar, ya karu da kaso 1.4 zuwa kaso 29 daga kaso 27.6 a rubu'i na 2 na bana, idan aka kwatanta da rubu'i na farko.

Hukumar ta ce matasan kasar ne suka mamaye kaso 63 na adadin marasa aikin yin.

Da take tsokaci game da alkaluman, jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance, ta ce matsalar rashin aikin yi ta zama annoba a kasar yanzu, la'akari da rashin ingantaccen tsarin yadda za a bunkasa tattalin arzikin kasar daga Gwamnati.

Jam'iyyar ta bukaci a kira taron muhawara na gaggawa game da matsalar rashin aiki a kasar.

A cewar Jam'iyyar, Afrika ta kudu na tsananin bukatar sauyi da tsarin da zai ingiza tattalin arzikin kasar shiga wani sabon babi, domin samar da yanayin da zai habaka harkokin kasuwanci da zuba jari hankali kwance.

A cikin manufarta ta raya kasa, gwamnatin kasar na da burin rage adadin matasa marasa aikin yi zuwa kaso 6, kawo shekarar 2030. Amma alkaluman na baya-bayan nan, sun nuna cewa Gwamnatin na da babban aiki a gabanta na cimma wannan buri. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China