Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CADF ya yi alkawarin zuba jari da samo kudi a Afrika da yawansa ya kai dala bilyan 29
2019-09-16 10:51:44        cri

An gudanar da dandalin zuba jari a nahiyar Afrika karo na biyar a Kongo Brazzaville, inda aka ba da labari cewa, asusun raya Sin da Afrika wato CADF ya zuba jarin da ya kai dala biliyan 5 a kasashen Afrika 36, matakin da ya ingiza kamfanonin Sin da su zuba jari da janyo kudi a Afrika da yawansa ya kai dala biliyan 24, ayyukan da suka amfanawa miliyoyin jama'ar Afrika.

Ma'aikatar kudi da bankin bunkasuwa na kasar Sin da gwamnatin kasar Kongo Brazzaville da bankin duniya ne suka shirya dandalin da aka gudanar a wannan karo.

CADF a matsayinsa na asusun hannun jari na farko, a cikin shekaru 12 da suka gabata, asusun ya hada kan bankin raya kasar Sin, inda suka taimakawa kamfanonin kasar Sin su shiga nahiyar Afrika da gaggauta raya fannonin arzikin Afrika a dukkanin fannoni ta hanyar hada-hadar kudi na zamani, da ingiza bunkasuwar tattalin arzikin Afrika ta hanyar zuba jari, ta yadda za a samar da karin guraben aikin yi da kara samun kudin haraji da kara fitar da kayayyaki. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China