Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da taron koli na Rasha da Afrika karo na farko a Sochi
2019-10-24 10:37:10        cri

An gudanar da taron koli na Rasha da Afrika karo na farko a Sochi na kasar Rasha a jiya Laraba. Yayin taron, an mayar da hankali ne game da hadin gwiwar Rasha da Afrika a fannin tattalin arziki da tsaro da dai sauransu.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya halarci taron dandalin tattalin arzikin Rasha da Afrika da aka shirya a wannan rana, inda ya nuna cewa, bunkasuwar nahiyar Afrika tana baiwa Rasha dammamakin hadin gwiwa masu dimbin yawa, ana sa ran yawan kudin dake shafar cinikayyar bangarorin biyu zai ninka cikin shekaru 4 ko 5 masu zuwa. Gwamnatin Rasha za ta ingiza kamfanonin kasar da su hada kai da Afrika. Ban da wannnan kuma, Rasha ta yafe basussukan da take bin Afrika na dala biliyan 20.

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sisi, wanda ke rike da shugabancin karba-karba na AU, ya ce, Afrika tana shiga wani muhimmin lokaci na bunkasuwa saboda ganin sauyi mai yakini da ake da shi a fannin kasuwanci da zuba jari da kuma boyayyen karfi da Afrika ke da shi ta fuskar masana'antu. Kasashen Afrika na fatan kara hadin gwiwa da kasar Rasha don daga matsayinta na tattalin arziki da boyayyen karfin kimiya da fasaha, da tabbatar da juyin juya hali kan masana'antu da kyautata manyan ababen more rayuwa. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China