Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jamiin Afrika ta kudu ya ce Tarzomar da aka yi bai kasance matakin nuna kiyayya ga baki ba
2019-09-11 10:17:58        cri

Ministan tsaron kasar Afrika ta kudu Nosiviwe Mapisa-Nqakula ya bayyana a jiya Talata cewa, tarzomar da aka yi tun daga karshen watan Agusta ba matakin nuna kyama ga baki ba ne.

Yayin da yake tsokaci kan lamarin a zaman zauren majalisar dokokin kasar da aka yi a Cape town, ya ce, mutane 12 sun rasa rayukansu cikin tarzomar, kuma 10 daga cikinsu 'yan Afrika ta kudu ne. Ya kara da cewa, yayin da aka tayar da zaune tsaye a kasar, an kwashi ganima da lahanta kantunan da 'yan kasar Afrika ta kudu suka mallaka. Ya zuwa yanzu dai, an kwantar da hankali a Johannesburg, Pretoria and Ekhurleni da dai sauran wurare. 'Yan sanda kuma na kokarin maido da zaman oda da doka a wasu wurare mafi samun tarzoma. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China