Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan samarwa kasashen Afrika karin damammaki
2019-10-18 19:39:54        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya shaidawa taron manema labarai da aka saba yi a yau Juma'a cewa, a halin yanzu, Sin da kasashen Afrika na kokarin aiwatar sakamakon da aka samu a taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin kan kasashen biyu da raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" tare.

Sin na fatan zurfafa hadin kai da kasashen Afrika ta fuskar raya masana'antu, manyan ababen more rayuwa, zuba jari da ciniki da sauransu, da kara samarwa kasashen Afrika karin dammamaki masu kyau da amfanawa jama'ar kasashen biyu baki daya

Rahotanni na cewa,a ranar 16 ga wata ne, aka fara amfani da zangon farko na layin dogo tsakanin Nairobi da Malaba da wani kamfanin Sin ya gina. Sannan kuma Sin da Mauritius sun kulla wata yarjejeniyar ciniki ba tare da shinge ba a jiya Alhamsi. Game da ci gaban da aka samu a baya-bayan nan, Geng ya ce, sabon ci gaban da aka samu ya bayyana niyyar bangarorin biyu na hadin kai da cin moriya tare da samun ci gaba tare, matakan sun samu karbuwa sosai daga bangaren Afrika. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China