Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rashin kunya! Navarro ya yi karya cikin littafinsa
2019-10-21 14:22:19        cri

 

Ranar 16 ga wata, Peter Navarro, babban mai bada shawara ga shugaban kasar Amurka ta fuskar tattalin arziki ya zama wanda aka fi ambatar sunansa a shafukan manyan kafofin yada labarun Amurka, sakamakon karyar da ya yi cikin wani littafinsa mai ra'ayin kin jinin kasar Sin.

A cikin littafinsa mai taken "Death by China" wanda ya rubuta a shekarar 2011, Navarroya ya ruwaito kalaman Ron Vara mai tsattsauran ra'ayi kan kasar Sin don tabbatar da gaskiyar tunaninsa wato kasar Sin ta kawowa Amurka barazana ta fuskar tattalin arziki.

Amma Tom Bartlett, wani masani ne a jami'ar kasar Australia yayi bincike ya kuma gano cewa, wannan mista Ron Vara ba ya kasancewa a duniya. Kuma idan an sauya tsarin sunansa Ron Vara, sai zai koma Navarro ke nan.

Ya zuwa yanzu, fadar shugaban Amurka wato White House bata bayyana ra'ayi kan lamarin ba tukuna. Amma a cikin sanarwarsa, Navarro ya amince da lamarin, ya kuma ce, ya tsara sunan Ron Vara ne domin farantawa mutane rai kawai. Ya ji dadin ganin bayan shekaru da dama, an gano wannan abin dariya da ya boye cikin littafinsa.

Dangane da hakan, Tom Bartlett ya ce, Navarro ya yi soke-soke kan kasar Sin da jama'ar Sin, don haka, bai yi abin dariya ba. Abin da Ron Vara ya fada yana da matukar muhimmanci, da kyar za a iya mayar da lamarin kamar wani abin dariya. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China