Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Liu He ya gana da jami'an kungiyoyin kasa da kasa da wakilan sassan masana'antu da cinikayya na Amurka
2019-10-11 10:46:55        cri
A ranar 9 ga wata da yamma, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kuma mataimakin firaministan kasar, kana jagoran shawarwarin tattalin arziki dake tsakanin Sin da Amurka Liu He, ya gana da shugaban kwamitin kula da harkokin ciniki da ke tsakanin Sin da Amurka Craig Allen, da zaunannen mataimakin shugaban majalisar harkokin ciniki ta kasar, kana shugaba mai kula da harkokin kasa da kasa Myron Brilliant, da kuma sabuwar shugabar asusun ba da lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva, a birnin Washington, fadar mulkin kasar Amurka.

A yayin ganawar tasu, Liu He ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan yin shawarwari da kasar Amurka kan batun daidaituwar ciniki da wasu harkokin dake jan hankulan kasashen biyu, domin cimma sakamako mai gamsarwa. A nasu bangare kuma, Craig Allen da Myron Brilliant sun bayyana fatansu na samu ci gaba a shawarwari na wannan zagaye, yayin kara fahimtar juna tsakanin kasashen biyu, don share fagen shawarwarin da za a gudanar a zagaye na gaba, ta yadda za a gano baki zaren warware sabanin dake tsakaninsu da kuma dakatar da takaddamar ciniki dake tsakanin kasashen biyu.

Cikin ganawarsa da Kristalina Georgieva, Liu He ya bayyana cewa, kasar Sin tana son cimma ra'ayi daya da kasar Amurka kan wasu batutuwan da suka dauki hankalin kasashen biyu bisa ka'idar mutunta juna da adalci, domin hana karuwar sabanin dake tsakaninsu. A nata bangare kuma, malama Georgieva ta ce, Asusun IMF yana yabawa matuka da kokarin da Sin ta yi wajen warware sabanin dake tsakaninta da Amurka ta hanyar yin shawarwari, kuma yana son ba da gudummawa yadda ya kamata kan harkokin kiyaye tsarin cinikin dake tsakanin bangarori daban daban da kuma kare ka'idojin ciniki cikin 'yanci. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China