Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Amurka ya gana da Liu He
2019-10-12 10:15:09        cri
Jiya jumma'a, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gana da mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kuma mataimakin firaministan kasar, kana jagoran shawarwarin tattalin arziki dake tsakanin Sin da Amurka Liu He a fadar White House ta kasar Amurka, a lokacin da ake gudanar da sabon zagayen taron shawarwari kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan kusoshin Sin da Amurka a Washington DC, fadar mulkin kasa ta Amurka.

Liu He ya mika sakon shugaban kasar Sin Xi Jinping ga Donald Trump, inda shugaba Xi ya ce, tawagogin tattalin arziki da cinikayya na kasashen biyu sun sami ci gaba kan shawarwarin da suka yi, ya kamata bangarorin biyu su warware matsalolin dake jan hankulansu yadda ya kamata, da kuma dukufa wajen cimma nasara a sauran fannoni, domin raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin yanayi mai kyau, tare da tallafawa kasa da kasa baki daya.

Mr. Trump ya yi godiya ga sakon da shugaba Xi ya kai masa. Ya kuma bayyana cewa, ya yi farin ciki da ganin ci gaban shawarwarin tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka, yana mai cewa, wannan abu ne mai kyau ga kasashen Sin da Amurka, har ma ga dukkanin kasashen duniya. Yana fatan tawagogin kasashen biyu za su ci gaba da dukufa kan wannan aiki, domin fidda sanarwa a hukumance game da shawarwarin da suka yi da kuma ciyar da shawarwari na nan gaba gaba kamar yadda ake fata.

Daga ranar 10 zuwa ranar 11 ga watan nan da muke ciki, tawagogin kasashen biyu suka yi taron shawarwari kan tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan kusoshin Sin da Amurka a Washington DC na kasar Amurka. Bangarorin biyu sun yi tattaunawa kan aikin gona, da kare 'yancin mallakar fasaha, da sha'anin harhadar kudi da kuma habaka hadin gwiwar ciniki da dai sauran harkoki, inda suka kuma cimma sakamako masu gamsarwa da dama. A sa'i daya kuma, sun tattauna kan gudanar da taron shawarwari na gaba, da kuma cimma matsaya daya kan dukufa wajen kulla wata yarjejeniya kan batun a hukumance. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China