Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yarjejeniyar ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka na da babbar ma'ana
2019-10-15 19:37:39        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya shaidawa manema labarai da aka saba yi a birnin Beijing a yau Talata cewa, yarjejeniyar ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka na da babbar ma'ana, kuma za ta amfanawa Sin da Amurka da daukacin duniya gaba daya, har ma da ba da gudummawa ga harkokin ciniki da tattalin arziki da tabbatar da zaman lafiya a duniya.

A kwanakin nan ne, aka gudanar da shawarwari tsakanin manyan jami'an Sin da Amurka karo na 13 a Washington DC. Amurka ta ce, bangarorin biyu sun kai ga cimma yarjejeniya a mataki na farko. A nata bangare kuma, Sin ta ce, kasashen biyu sun samu sakamako mai kyau a wasu fannoni, sun kuma amince za su yi kokarin hada kai wajen ganin sun cimma yarjejeniya ta karshe. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China