Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata a cimma matsaya daya tare kuma da girmama ra'ayoyi daban daban
2019-10-12 10:41:35        cri
An kammala sabon zagayen karshen taron shawarwarin tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan kusoshin Sin da Amurka a Washington DC, fadar mulkin kasa ta Amurka jiya Jumma'a, inda aka kuma cimma sakamako masu gamsarwa da dama. Kana, sun tattauna kan taron shawarwari da za a yi a nan gaba.

Shawarwarin da kasashen biyu suka yi bisa ka'idar neman cimma matsaya daya tare kuma da girmama ra'ayoyi daban daban zai ba da gudummawa wajen magance tsanantar takaddamar ciniki dake tsakanin kasashen biyu.

Hadin gwiwar Sin da Amurka za ta tallafawa kasashen biyu, kuma tabbas, yake-yaken dake tsakaninsu za su haifar da illa ga kasashen biyu. Kasar Sin tana fatan warware sabanin dake tsakanin kasashen biyu ta hanyar yin shawarwari da hadin gwiwa cikin ruwan sanyi, amma kuma ba za ta yi rangwame ko kadan kan muhimman muradun kasar ba.

Bugu da kari, ba tare da la'akari da sauye-sauye a duniya ba, kasar Sin za ta ci gaba da zurfafa aikin yin kwaskwarima da kuma kara bude kofa ga waje, domin kokarin samun bunkasuwar tattalin arziki mai inganci. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China