Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta yi Allah wadai kan yadda Amurka ta takaita fitar da kayayyaki ga hukumar 'yan sandan jihar Xinjiang
2019-10-10 11:17:36        cri
Jiya Laraba, ofishin yaki da ta'addancin kasar Sin ya fidda wata sanarwa, inda ya yi Allah wadai da kakkausan harshe kan ma'aikatar kasuwancin kasar Amurka, bisa yadda ta sanya hukumar 'yan sandan jihar Xinjiang ta kasar Sin, da sauran hukumomin kasar cikin jerin sunayen hukumomin da Amurka za ta takaita sayar musu da kayayyaki.

Ofishin yaki da ta'addancin kasar ya kuma bayyana cewa, hukumomin tsaron jama'a na yankin Xinjiang suna gudanar da ayyukansu bisa dokokin kasar Sin yadda ya kamata, sun kuma dukufa wajen yaki da 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'yi, don neman dakile ayyukan ta'addanci a jihar, da kuma kare zaman lafiya da zaman karko na al'ummomin Xinjiang, lamarin da ya sa suke samun goyon baya daga wajen jama'ar jihar da yawansu ya kai miliyan 25. Sun kuma bada babbar gudummawa cikin aikin yaki da ta'addanci na kasa da kasa, inda suke samun yabo daga gamayyar kasa da kasa.

A cikin sanarwar, an kara da cewa, yanzu ana samun ci gaban tattalin arziki, zaman lafiyar jama'a da kyautatuwar zamantakewar al'umma a jihar Xinjiang kamar yadda ake bukata, sa'an nan mutane na kabilu daban daban suna zama a jihar cikin annashuwa, inda suke jin dadin zaman rayuwarsu matuka.

Bugu da kari, ofishin yaki da ta'addancin kasar Sin ya ce, bai kamata kasar Amurka ta nuna bambanci kan batun yaki da ta'addanci ba, kuma ya kamata ta daina tsoma baki cikin harkokin jihar Xinjiang na kasar Sin. An bukaci Amurka da ta dakatar da nuna goyon baya ga kungiyar 'yan ta'adda ta Turkestan ta Gabas, don wani dalili na son kai. Sin tana kuma kalubalantar kasar Amurka da ta gyara kuskurenta, kana ta dakatar da tsoma baki a harkokin cikin gida na kasar Sin.

A nan gaba kuma, kasar Sin zata dauki matakai yadda ya kamata wajen yaki da ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi domin kiyaya zaman karko a Xinjiang, da kokarin kare cikakken yankin kasa da kuma cigaban kasa baki daya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China