Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin a Najeriya ya fidda sharhi mai taken "kawar da talauci da kiyaye hakkin dan Adam"
2019-10-18 10:57:03        cri

Ranar 17 ga watan Oktoba rana ce ta "kawar da talauci" ta kasa da kasa. Jaridar Jama'a ta kasar Najeriya ta gabatar da sharhi mai taken "kawar da talauci da kiyaye hakkin dan Adam" wanda jakadan kasar Sin dake Nijeriya Zhou Pingjian ya rubuta. Cikin wannan sharhi, jakada Zhou ya bayyana cewa, a lokacin da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949, kasar Sin ita ce daya daga cikin kasashe mafi fama da talauci. Amma, bisa jagorancin da shugabannin kasar Sin suka yiwa al'ummomin kasar cikin shekaru 70 da suka gabata, ma'aunin tattalin arzikin GDP na kasar Sin ya karu da kashi 4.4% cikin kowace shekara a farkon shekaru 30 cikin wadannan shekaru 70, sa'an nan, ya karu da kashi 9.5% cikin kowace shekara a karshen shekaru 40 cikin wadannan shekaru 70. Don haka, matalauta masu dimbin yawa sun kawar da talaucinsu.

A halin yanzu, kasar Sin ta kasance kasar da ta fi fitar da yawan al'umma daga kangin talauci a fadin duniya, kuma ita ce kasa ta farko da ta cimma muradun kawar da talauci da samun bunkasuwa na MDD cikin dukkanin kasashe masu tasowa a duniya. Ta kuma bada gudummawa ta 70% cikin aikin kawar da talauci na kasa da kasa. Kana, ya zuwa shekarar 2020, Sin za ta kawar da talauci a duk fadin kasar gaba daya.

A cikin sharhin an kuma ce, cikin jawabin da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar a watan Yuni na bana, yana mai cewa, kasar Nijeriya zata fitar da matalauta kimanin miliyan dari 1 daga kangin talauci cikin shekaru 10 masu zuwa, bisa jagoranci mai karfi da kudurin da muka tsaida.

Mun yaba matuka dangane da kokarin da kasar Najeriya ta yi domin bada karin gudummawa cikin aikin kawar da talauci na kasa da kasa, kuma ana imanin cewa, tabbas ne kasar Najeriya zata cimma burinta na kawar da talauci.

A sa'i guda kuma, kasar Sin tana son yin hadin gwiwa da kasar Najeriya da ma sauran kasashen duniya kan aikin kawar da talauci, domin samun bunkasuwar kasa da kasa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China