Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta lashi takobin dakile hare-haren da ake kai wa makarantu a jihar Kaduna
2019-10-12 16:28:13        cri
Rundunar 'yan sandan Nijeriya, ta ce tana kokarin yin dukkan mai yuwuwa wajen kawo karshen hare-haren da bata gari ke kaiwa makarantun jihar Kaduna a baya-bayan nan.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Kaduna dake arewacin kasar, Ali Janga, wanda ya bada tabbacin cikin wata sanarwa da ta shiga hannun kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce jami'an tsaro na aiki ba dare ba rana domin dakile sabon salon da bata gari suka dauka na kai hari kan masu rauni.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa Xinhua cewa, a ranar Alhamis da ta gabata, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba, sun kai hari wata makarantar sakandare ta jihar, inda suka sace shugaban makarantar.

Lamarin ya zo ne kasa da mako guda, bayan an sace wasu dalibai mata 6 da malamai 2 na kwalejin Engravers dake yankin Chikun na jihar.

Ali Janga ya ce 'yan sanda za su kare sake aukuwar wannan lamari, yana mai kira ga iyaye, da kada su bari hare - haren su sanyaya musu gwiwa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China