![]() |
|
2019-10-09 10:08:28 cri |
Yayin da suke tabbatar da lamarin da ya auku a unguwar Pegi na yankin Kuje, 'yan sanda sun ce ana kokarin ceto mutanen.
Kakakin rundunar 'yan sanda birnin Abuja, Anjuguri Manzah, ya ce ana gudanar da bincike domin gano 'yan bindigar.
Ya kara da yin kira ga jama'a, da su yi taka-tsantsa tare da bayar da rahoton duk wata zirga-zirga ko ayyukan da basu yarda da su ba a yankunansu, ga 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
Wata kafar yada labarai ta kasar, ta ce wani yaro mai shekaru 12 na daga cikin mutanen da aka sace.
A cewar mazauna yankin, 'yan bindigar sun kafa wani shingen bincike, inda suka ba mutanen umarnin sauka daga mota. Daga nan kuma suka sanya su cikin wata mota ta daban, tare da yin awon gaba da su, zuwa wani wuri da ba sani ba. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China