Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya za ta kara farashin gangar danyen man fetur zuwa dala 57
2019-10-09 11:29:05        cri

Gwamnatin Nijeriya ta gabatar da bukatar kara farashin danyen man fetur, daga dala 55 zuwa dala 57 kan kowacce gangar mai.

Shugaban Kasar Muhammadu Buhari ne ya sanar da haka a jiya, lokacin da yake gabatar da kudurin kasafin kudin badi ga zaman hadaka na majalisun dokokin kasar.

Wannan shi ne zai kasance farashi ga masu saye da sayar da danyen man kasar.

A cewar shugaba Buhari, za a yi amfani da ribar karin ne wajen biyan albashi ma'aikata da kuma albashin jami'ai 30,000 da ake son dauka a rundunonin soji da 'yan sanda, da hukumar kula da shige da fice da hukumar tsaro ta Civil Defence na kasar.

Kwararru a kasar sun yi fatan kara farashin da aka yi a bara daga dala 45 zuwa 50.5, zai karawa al'ummar kasar kwarin gwiwar samun kyautatuwar al'amura da bunkasa tattalin arzikin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China