![]() |
|
2019-10-16 10:37:17 cri |
Shugaban kamfanin na NNPC, Mele Kyari, ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa, akwai yuwuwar cimma burin, saboda shirye shiryen da gwamnati ke gudanarwa.
Ya ce ana gudanar da shirye shirye, ciki har da fadada shiga sabbin wuraren hakar mai, wanda ya kai su ga sanar da gano man fetur a tafkin Gongola, yana ma cewa suna sa ran samun wasu kari.
Gwamnatin kasar ta gabatar da kudurin kasafin kudin shekarar 2020, wanda ya ke sa ran samar da gangar miliyan 2.18 a kowacce rana.
Bangaren man fetur na taka muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin kasar. Bisa jawabin da shugaban kasar Muhammadu Buhari ya gabatar dangane da kasafin kudin, daga cikin naira triliyan 8.155, kwatankwacin dala biliyan 23 na kudin shigar da aka yi hasashen samu a shekarar 2020, wanda za ta samu daga bangaren mai ya tsaya kan naira triliyan 2.64. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China