Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gayyaci dabilai su ziyarci ofishin jakadancin Sin dake Nijeriya
2019-09-26 15:08:48        cri

A jiya ne, domin murnar ranar kafuwar sabuwar kasar Sin, ofishin jakadancin Sin dake Nijeriya, ya gayyaci malamai da dalibai na makarantar firamare ta sada zumunta a tsakanin Sin da Nijeriya ta birnin Abuja don su ziyarci ofishin, inda jakadan Sin Zhou Pingjian ya yi hira da su tare da bada lambobin yabo na sada zumunta da murnar ranar kafuwar sabuwar kasar Sin ga dalibai 48.

Jakada Zhou Pingjian ya bayyana cewa, ranar 1 ga watan Oktoba na bana rana ce ta cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin, kana rana ce ta cika shekaru 59 da samun 'yancin kan kasar Nijeriya. A cikin shekaru 48 da aka kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Nijeriya, an samu nasarori da dama kan hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu a fannonin bada ilmi da sauransu. Yana fatan dalibai za su kara samun ci gaba a karatu, da kasancewa masu sada zumunta tsakanin kasashen biyu.

Direktan kwamitin kula da bada ilmi na yankin FCT na kasar Nijeriya ya bayyana cewa, an samu babbar nasara kan gina makarantar firamare ta sada zumunta a tsakanin Sin da Nijeriya bisa goyon bayan ofishin jakadancin Sin dake Nijeriya, gwamnatin yankin tana yada fasahohin da aka samu a wannan fanni ga sauran makarantu. Ya kuma godewa gwamnatin kasar Sin domin ta nuna goyon bayan sha'anin bada ilmi na kasar Nijeriya, tare da taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar sabuwar kasar Sin. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China