Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Nijeriya ta samu jarin dala biliyan 9.29 daga kasashen ketare a rubu'i na 3 na bana
2019-10-12 16:44:55        cri
Hukumar bunkasa harkokin zuba jari ta Nijeriya NIPC, ta ce kasar ta samu jarin da ya kai dala biliyan 9.29 daga kasashen waje a rubu'i na 3 na bana.

Yayin wani taron manema labarai jiya a Abuja babban birnin kasar, shugabar hukumar Yewande Sadiku, ta ce bangaren hakar ma'adinai da duwatsu ne ya mamaye kaso 98 cikin 100 na jimilar jarin.

Ta ce bangaren sadarwa da na hada-hadar kudi da inshora da na sufuri da na gidaje da bangaren kiwon lafiya da na hidimomin jama'a da na sarrafa kayayyaki da na ayyukan gona ne suka dauki ragowar kaso 2 na jimilar adadin.

Ta kuma bayyana yankin Neja Delta a matsayin wurin da ya dauki kaso 87 na jari, sai kuma jihar Kaduna dake arewaci kasar da jihohin Lagos da Anambra da Ogun na kudancin kasar da suka samu kasa da kaso 1 kowannensu.

Har ila yau, ta ce gwamnatin kasar na daukar matakan da suka dace na kara jan hankalin masu zuba jari na ketare, domin bunkasa tattalin arzikinta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China