Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta nuna damuwa kan halin da arewa maso gabashin Syria ke ciki
2019-10-17 10:49:27        cri

A ranar 16 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya kira taron yin shawarwari kan yanayin da arewa maso gabashin kasar Syria ke ciki. Shugaban kwamitin, kana zaunannen wakilin kasar Afirka ta Kudu a MDD Jerry Matjila ya bayyana bayan taron cewa, mambobin kwamitin sulhu na MDD sun nuna damuwarsu matuka kan yanayin da yankin arewa maso gabashin kasar Syria yake ciki, saboda a halin yanzu, 'yan ta'adda sun bazu a ko ina a wannan yanki, kuma ana fuskantar tabarbarewar yanayin jin kai a kasar Syria.

Bayan taron, zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Zhang Jun ya bayyana cewa, kasar Sin tana maida hankali matuka kan yanayi da yankin arewa maso gabashin kasar Syria ke ciki, ya kamata a kiyaye 'yancin kai da cikakken yankunan kasar Syria da ma dinkuwarta yadda ya kamata. Kuma hanyar siyasa a maimakon hanyar soja ita ce hanya kadai mafi dacewa wajen warware matsalar Syria. Shi ya sa kasar Sin ta yi kira ga kasar Turkiyya da ta dakatar da matakan soja data dauka a kasar Syria, tare kuma da dawo hanyar warware matsalar ta hanyar siyasa.

Ya kara da cewa, bangarorin kasar Syria sun cimma ra'ayi daya kan kafa kwamitin tsarin mulkin kasa kwanan baya. Kasar Sin tana goyon bayan MDD da ta gaggauta aiwatar da kuduri mai lamba 2254 da kwamitin sulhu na MDD ya tsaida, da kuma tsara daftarin warware batun Syria ta hanyar siyasa da zai iya kiyaye moriyar bangarorin da abin ya shafa. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China