Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Turkiya ta fara aiwatar da matakan soja a arewacin Syria
2019-10-10 11:18:21        cri

A daren jiya Laraba, ma'aikatar tsaron kasar Turkiya ta sanar cewa, rundunar sojojin kasar sun fara daukar matakan soja kan kungiyar Kurdish dake arewacin kasar Syria.

Wani sojan kasar Turkiya ya bayyana cewa, bayan kai hare-hare ta sama da harba boma-bomai na awo'i da dama a kasar Syria, sojojin kasa na kasar Turkiya sun shiga cikin garin Ras al-Ayn da garin Tal Abyad dake yankin kan iyakar kasar Syria ta hanyoyi hudu.

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana a ranar 5 ga wata cewa, kasarsa za ta dauki matakan soja kwanan baya, domin kashe masu daukar makamai na kungiyar Kurdish dake yankin iyakar kasar Syria, da kuma kafa "yankin tsaro" cikin kasar ta Syria.

Sa'an nan, a ranar 6 ga wata, gwamnatin kasar Amurka ta bayyana cewa, ba ta goyi bayan matakan Turkiya na shiga cikin kasar Syria ba, kuma za ta janye jiki daga yankin da abin ya shafa.

Kana, gwamnatin kasar Syria tana daukar matakan soja da kasashen Amurka da Turkiya suka aiwatar cikin kasarta a matsayin keta ikon kasar ta Syria, kuma ta yi Allah wadai da wannan batu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China