Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaba Syria ya zargi kasashen yamma da hana 'yan kasar dake gudun hijira dawowa gida
2019-09-23 10:31:46        cri

Shugaba Bashar al-Assad na kasar Syria, ya zargi kasashen yammacin duniya, da yunkurin hana 'yan kasar dake gudun hijirar kasar dawowa cikin kasar.

Shugaba Assab ya bayyana hakan ne, yayin wata ganawa da ya yi da wata tagawar 'yan siyasa da masu tsara dokoki daga kasar Italiya karkashin jagoranci senata Paolo Romani a Damascus, babban birnin kasar.

Kamfanin dillancin kasar Syria, SANA ya ruwaito shugaban na fada cikin wani rahoto cewa, matsayin galibin kasashen Turai game da halin da ake ciki a kasar Syria, ya sha bamban da ainihin abin da ke faruwa, tun lokacin da fada ya barke a kasar sama da shekaru 8 da suka gabata.

Shugaba Assad ya ce, kasashen Yamma, musamman Amurka da Turkiya, har yanzu su ke kawo cikas a kokarin da ake yi na kawar da ayyukan ta'addanci, da ma hana 'yan kasar dake gudun hijira dawowa gida.

A nasu bangare, mambobin tawagar kasar ta Italiya, sun bayyana cewa, ya kamata gwamnatocin kasashen Turai, su bullo da wata manufa game da abubuwan dake faruwa a Syria bisa hakikanin gaskiya maimakon rahotannin karya da kafafen yada labarai ke watsawa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China