Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta nemi samun damar kai agajin jin kai arewacin Syria
2019-10-11 11:40:02        cri
MDD ta nemi samar da agajin jin kai ga dubban jama'ar da suka tserewa rikici, da kara shiga mawuyacin hali ta hanyar zama cikin sanyi a arewacin Syria.

A ranar Laraba da ta gabata ne Turkiyya ta kaddamar da ayyukan soji a arewacin Syria.

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq, ya shaidawa manema labarai cewa, babban kwamishinan hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar, ya jaddada bukatar gaggauta samun damar kai agajin jin kai ga mutanen da suka rasa matsugunansu tare da taimaka musu.

A nata bangaren, Henrietta Fore, Babbar Daraktar asusun kula da kananan yara na MDD UNICEF, ta bukaci dukkan bangarori su kare yara da ababen more rayuwa da suka dogara da su, kamar yadda dokokin jin kai da na hakkin bil adama suka tanada. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China