Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka za ta janye sojojinta daga arewacin Syria
2019-10-14 12:37:12        cri

Sakataren tsaron kasar Amurka Mark Esper, ya ce Amurka na shirin janye sojojinta kimanin 1,000 daga arewacin Syria, inda dakarun kasar Turkiyya ke kai hari kan mayakan Kurdawa.

Mark Esper, ya bayyana cewa, cikin sa'o'i 24 da suka gabata, sun samu labarin cewa, dakarun Turkiyya za su ci gaba da fadada kai hare-hare zuwa yankunan kudu da yammacin kasar, sabanin yadda suka tsara a baya.

Ya bayyana yanayin a matsayin mai sarkakkiya, la'akari da yadda ya rutsa da sojojin Amurka a tsakiyar abokan adawa.

Ya kara da cewa, ya tattauna da shugaban kasar, bayan ya tuntubi sauran tawagar tsaron kasar, inda shugaban ya bada umarnin fara janye sojojin daga arewacin Syria, yana mai tabbatar da cewa, adadin dakarun ya kai 1,000.

Sai dai, Mark Esper bai bayyana ainihin lokacin da za a fara janye sojojin ba, amma ya ce za a gudanar da aikin cikin sauri da kuma aminci. (Fa';iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China