Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Syria ta soki Turkiyya saboda kai hari kan fararen hula a arewacin kasar
2019-10-11 13:50:19        cri

Kamfanin dillancin labarai na kasar Syria wato SANA, ya ruwaito ma'aikatar harkokin wajen kasar na yin tir da ayyukan sojojin Turkiyya a arewacin kasar.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta ce ayyukan da sojojin Turkiyya suka fara a ranar Laraba da sunan yaki da ta'addanci, na rutsawa da fararen hular da ba su ji ba, ba su gani ba a arewacin kasar.

Sanarwar ta ce kare al'ummar Syria, hakki ne na sojojin kasar kadai, tana mai jaddada cewa, za a dauki dukkan matakan dake akwai wajen tunkarar harin na Turkiyya .

A ranar Laraba ne Turkiyya ta sanar da fara ayyukanta na soji da ta dade tana barazanar aiwatarwa a arewacin Syria, da nufin fatattakar mayakan Kurdawa da kuma uwar kungiyar mai rajin kare jama'a wato People's Protection Units, wadanda Turkiyyar ta dauke su a matsayin 'yan aware kuma 'yan ta'adda. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China