Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi maraba da kafuwar kwamitin kula da harkokin kundin tsarin mulkin kasar Syria
2019-10-09 13:37:46        cri

Jiya Talata ne kwamitin sulhu na MDD ya ba da wata sanarwa, inda ya yi maraba da kafuwar kwamitin kula da harkokin kundin tsarin mulkin kasar Syria, yana kuma goyon bayan MDD da ta shirya taro karo na farko na kwamitin kula da harkokin kundin tsarin mulkin kasar Syria kafin ranar 30 ga wata a Geneva.

Sanarwar ta ce, kwamitin sulhun na ganin cewa, kafa kwamitin kula da harkokin kundin tsarin mulkin kasar Syria da ke karkashin shugabancin al'ummar Syria, zai kasance wani mafari na ayyukan siyasa na kawo karshen rikicin Syria bisa kuduri mai lamba 2254 da kwamitin sulhu ya tsai da. Kana kuma kwamitin sulhun ya sake nanata cewa, bai kamata a kawo karshen rikicin Syria ta hanyar karfin soja ba, maimakon haka, a sa aya ga rikici bisa kudurin mai lamba 2254 na kwamitin. Kwamitin sulhu ya sake jaddada alkawarinsa na kiyaye ikon mulkin kasar ta Syria da 'yancin kanta da dinkewarta da cikakkun yankunanta. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China