Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta kara bude sana'ar hada-hadar kudi ga kasashen waje
2019-10-16 14:54:08        cri

Jiya Talata, gwamnatin kasar Sin ta gabatar da kudurin gyara "tanade-tanaden gudanarwar harkokin kamfanonin ba da inshora masu jarin waje na jamhuriyyar jama'ar kasar Sin" da kuma "tanade-tanaden gudanarwar harkokin bankuna masu jarin waje na jamhuriyyar jama'ar kasar Sin", domin kara bude sana'ar banki da sana'ar ba da inshora ga kasashen waje, da kuma kiyaye moriyar kamfanoni masu jarin waje yadda ya kamata.

Maryam Yang na dauke da karin bayani…

Gwamnatin kasar Sin ta fitar da "tanade-tanaden gudanarwar harkokin kamfanonin ba da inshora masu jarin waje na jamhuriyyar jama'ar kasar Sin" a shekarar 2001 da kuma "tanade-tanaden gudanarwar harkokin bankuna masu jarin waje na jamhuriyyar jama'ar kasar Sin" a shekarar 2006, domin cika alkawarin da ta yiwa kungiyar cinikayya ta duniya, wato WTO, Sin ta gudanar da ayyukan da gamayyar kasa da kasa suka ba ta bisa dokokin kasar.

Jiya Talata, babban lauya na kwamitin sa ido kan harkokin bankuna da ba da inshora na kasar Sin Liu Fushou ya bayyana a taron manema labaran da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira cewa, an gyara wasu sharruda na "tanade-tanaden gudanarwar harkokin kamfanonin ba da inshora masu jarin waje" da "tanade-tanaden gudanarwar harkokin bankuna masu jarin waje" bisa kudurin da kwamitin tsakiyar Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin da majalisar gudanarwar kasa suka tsaida, domin kara bude sana'ar hada-hadar kudi ta kasar Sin ga kasashen waje, da kuma samar da dokokin da za su dace wajen kare moriyar kamfanoni ba da inshora masu jarin waje da kuma moriyar bankuna masu jarin waje.

Ya kara da cewa, an gyara "tanade-tanaden gudanarwar harkokin bakuna masu jarin waje" a fannoni guda hudu, ya ce, "Da farko, samar da sauki ga masu zuba hanayen jari da suke son kafa bankuna masu jarin waje a kasar Sin, da bankunan waje da suke son kafa reshensu a kasar Sin. Na biyu shi ne, samar da sauki ga bankunan waje da suke son kafa wakilai bankuna da reshensu a lokaci guda a kasar Sin. Na uku shi ne, rage kayyaden dake tattare da bankuna masu jarin waje. Na hudu shi ne, daidaita bukatun da aka yiwa bankunan waje kan kudaden da za su adana."

Ban da haka kuma, cikin gyaran da Sin ta yi kan "tanade-tanaden gudanarwar harkokin kamfanonin ba da inshora masu jarin waje", ta soke wasu sharrudan shigar da kamfamonin ba da inshora masu jarin waje a kasar Sin, ciki har da, sharadi na "gudanar da harkokin ba da inshora sama da shekaru 30" da na "kafa ofishinsa a kasar Sin sama da shekaru 2". Daga bisani kuma, Sin ta yarda da hadadden kamfanonin ba da inshora na kasashen waje da su kafa kamfanonin ba da inshora masu jarin waje a kasar Sin, kuma za ta amince hukumomin hada-hadar kudi na kasashen katare su samar da jari ga kamfanonin ba da inshora masu jarin waje.

Liu Fuzhou ya bayyana cewa, gyaran da Sin ta yi kan tanade-tanaden biyu ta soke wasu sharruda na shigar da bankuna da kamfanonin ba da inshora masu jarin waje cikin kasar Sin, da kuma samar da sauki gare su wajen kafa kamfanoni masu jarin waje a kasar Sin, lamarin da ya janyo hankulan karin kamfanonin kasashen ketare masu zuba jari a kasar Sin.

"Sin ta samar da karin damammaki ga kamfanonin ketare da su kafa reshensu a kasar, saboda sharruda da dama da ta soke. Kuma bisa ka'idar adalci da cimma moriyar juna, kasar Sin tana maraba da zuwan karin kamfanonin hada-hadar kudi a kasar Sin, domin samar da karin hajoji da kuma ba da hidima a kasuwannin hada-hadar kudi, da kuma ba da tallafi ga kamfanoni da al'ummomin kasar ta Sin."

Haka zalika, Liu Fuzhou ya ce, babbar ka'idar da muke bi a lokacin da Sin ta gyara tanade-tanaden nan biyu ita ce cimma moriyar juna, shi ya sa, Sin ba ta son nuna bambanci ga kamfanoni masu zaman kansu, da kamfanoni mallakar gwamnati da kuma kamfanoni masu jarin waje, domin su yi hadin gwiwa da takara cikin yanayin adalci, ta yadda dukkansu za su iya cimma moriya.

Bugu da kari, ya ce, kwamitin sa ido kan bankuna da kwamitin sa ido kan sana'ar ba da inshora za su samar da "bayanin yadda ake gudanar da harkokin bankuna masu jarin waje" da kuma "bayanin yadda ake gudanar da harkokin kamfanonin ba da inshora masu jarin waje" da dai sauran manufofi, domin tsara cikakken shirin bude kofa ga waje ta fuskar sana'ar hada-hadar kudi. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China