![]() |
|
2019-10-15 14:46:46 cri |
Za a gudanar da gasar wasannin sojoji ta kasa da kasa karo na 7 a birnin Wuhan na lardin Hubei daga ranar 18 zuwa 27 ga wata, wanna ne karo na farko da za a gudanar da irin wannan gasar wasannin aikin soja ta duniya a nan kasar Sin.
Da safiyar yau Talata ne aka shirya taron manema labaru a cibiyar kafofin yada labaru ta gasar wasannin sojoji ta kasa da kasa karo na 7, inda aka yi karin bayani kan yadda ake shirya bikin bude gasar.
An labarta cewa, za a tabo batutuwan sojoji, rundunoni, da al'adun aikin soja a yayin bikin bude gasar, a kokarin bayyana fatan al'ummar Sinawa na neman samun zaman lafiya tun fil azal har zuwa yanzu. (Tasallah Yuan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China