Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ana dab da bude taron baje kolin kayayyakin shige na duniya na kasar Sin karo na 2
2019-10-15 13:57:11        cri

Za a bude taron baje kolin kayayyakin shige na kasa da kasa na kasar Sin karo na 2 a ranar 5 ga watan Nuwamban bana. Yanzu an shiga mataki na karshe na shirya taron.

Za a ware sassa guda 7 na yayata kamfanonin da za su halarci taron a bana. Fadin sashen gwada injuna ya kai misalin murabba'in mita dubu 60 baki daya, inda kamfanoni fiye da dari 3 suka tabbatar da za su halarci taron a bana. Sa'an nan an kara wurin nune-nunen injuna a fili a bana, inda za a gwada yadda ake sarrafa kayayyaki, injuna, kayayyaki masu nasaba da jiragen sama, mutum-mutumin inji, kayayyaki masu sarrafa kansu, fasahar zamani, yadda ake tinkarar batutuwa daga dukkan fannoni da dai sauransu.

Haka zalika kuma, fadin sashen nune-nunen ingantuwar zaman rayuwar jama'a ya kai murabba'in mita dubu 63 baki daya, inda kamfanoni 880 daga kasashe da yankuna guda 86 za su gwada kayayyakin gida, kayayyakin masarufi, abubuwan gyara fuska, tufafi, da kayayyakin da iyaye mata da kananan yara suke amfani da su, kayayyakin masarufi masu daraja da kuma kayayyakin lu'ulu'u da dai makamantansu. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China