Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Liu He zai tafi Amurka don halartar shawarwarin tattalin arziki da cinikayya karo na 13 a tsakanin Sin da Amurka
2019-09-29 20:25:23        cri
Mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin, kuma mataimakin wakilin tawagar Sin dake kula da shawarwarin cinikayya na kasa da kasa, Wang Shouwen ya yi bayani yayin taron manema labaru game da bikin murnar cika shekaru 70 da kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin da aka shirya a yau Lahadi, inda ya ce a cikin makon da zai biyo bayan na bikin kasar, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana mataimakin firaministan gwamnatin kasar, kuma mai jagoran shawarwarin tattalin arziki tsakanin kasashen Sin da Amurka, Liu He zai jagoranci wata tawaga zuwa Washington, don yin shawarwarin tattalin arziki da cinikayya karo na 13 tsakanin Sin da Amurka.

Wang Shouwen ya ce, ba da dadewa ba, ministocin kasashen Sin da Amurka sun yi shawarwari a Washington, inda suka tattauna kan wasu muhimman batutuwan tattalin arziki da cinikayya dake jan hankulansu duka, da kuma wasu ayyukan da za a yi a gun shawarwarin tattalin arziki da cinikayya karo na 13. Wang ya ce, ko da yaushe kasar Sin na nuna tabbaci kan matsayinta game da shawarwarin, kuma ta sha jaddada manufarta irin ta nuna girmama juna, da zaman daidai wadaida, don neman dabarun warware matsaloli ta hanyar yin shawarwari cikin adalci. Wannan ya dace da moriyar kasashen biyu, da ta duniya baki daya. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China