Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gayyaci tawagar Sin dake tattauna batun kasuwanci da Amurka zuwa wani sabon zagayen tattaunawa
2019-10-08 10:31:43        cri
Bisa gayyatar da Amurka ta yi, mataimakin Firaministan kasar Sin Liu He, zai jagoranci tawagar kasar zuwa Washington na kasar Amurka, domin wani sabon zagayen tattauna harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakanin manyan jami'an kasashen 2 daga ranar 10 zuwa 11 ga wata.

Liu He, wanda mamba ne a hukumar kula da harkokin siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, kuma jagoran tawagar kasar Sin a tattaunawar tattalin arziki da cinikayya da take da Amurka, zai tattauna da jagoran tawagar bangaren Amurka Robert Lighthizer da kuma sakataren kudin kasar Steven Mnuchin. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China