Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin za ta kaucewa fito na fito da tabbatar da dangantakar moriyar juna tsakaninta da Amurka
2019-09-28 16:05:52        cri
Ministan harkokin wajen Sin Wang Yi, ya ce kasar Sin ta kuduri niyyar kaucewa rikice-rikice da fito-na-fito, tare da tabbatar da dangantakar moriyar juna tsakaninta da Amurka.

Da yake ganawa da Sakataren harkokin wajen Amurka, Henry Kissinger, Wang Yi ya ce, dangantakar Sin da Amurka ya kai wani mataki mai muhimmanci.

Ya ce abu ne mai hatsari wasu Amurkawa su rika kira da daukar Sin a matsayin abokiyar adawa, ko kuma neman raba dangantakar kasashen 2.

Wang Yi ya ce, Kasar Sin na fatan Amurka, za ta rungumi tsarin girmama bambancin dake tsakaninsu tare da aiki da kasar Sin domin daidaita sabanin ta hanyar girmama juna da karfafa dangantakar moriyar juna da hada hannu wajen raya dangantaka mai karfi a tsakaninsu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China